<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>327</hymn_number>
<title>Mun Kawo Ƴaƴanmu, Yesu LW327</title>
<lyrics>[V1]
 1) Mun kawo ƴaƴanmu, Yesu,
 Kai wanda ka ke ƙaunarsu.
 Ka ɗibiya musu hannunka,
 Ka sa musu albarkarka.

[V2]
 2) Ka tsare ƴaƴanmu, Yesu,
 Ka rungume su, dukansu,
 Kewaye su da ƙaunarka,
 Ka riƙe su da ikonka.

[V3]
 3) Kiyaye ƴaƴanmu, Yesu,
 Ka yafe musu laifinsu,
 Ka koya musu halinka,
 Ka cika su da Ruhunka.</lyrics>
</song>